Kamar yadda fadar shugaban Kasa ta sanar wa ‘yan Najeriya cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi yau, da karfe 7 na safiyar litinin Buhari ya yi jawabin in da a ciki ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su zauna tsintsaye madaurinki daya maimakon cecekuce da ake tayi na neman raba kasar.
Ga abin da Buhari ya ce.
‘Yan uwana ‘yan Najeriya. Ina mai godiya ga Allah da kuma daukacin ku ‘yan Najeriya saboda addu’o’in da kuka ta yi mini. Ina farin cikin dawowa gida cikin ku maza da mata.
Yayin da nake kasar Birtaniya, ina samun cikakken labaran abubuwan da ke faruwa a gida.
‘Yan Najeriya suna tattauna al’amuran da suke faruwa, amma na fahimci cewa wasu daga cikin kalaman da ake yi musamman a kafofin sada zumunta sun ketara iyakar dokokin kasar nan inda suke sanya alamar tambaya game da ci gaba da kasancewarmu kasa daya.
A shekarar 2003 bayan da na shiga siyasa, marigayi Emeka Ojukwu ya ziyarceni ya a Daura kuma mun kwashe fiye da kwana biyu muna tattauna matsalolin Najeriya, a wasu lokutan mukan shafe dare muna magana. A karshe mun cimma matsayar cewa wajibi ne Najeriya ta ci gaba da kasancewa kasa daya.
Hadin kan ‘yan Najeriya wani abu ne da aka cimma matsaya a kai. Kuma ba za mu ce za mu sake duba sa ba. Sannan ba za mu bari wasu wadanda ba su da kamun kai su fara tada fitina kuma idan abubuwa suka lalace su gudu su bar wasu da aikin dawo da doka da oda ba, wata kila ma hakan ba zai yiwu ba sai an zubar da jinin mutane.
Kowane dan Najeriya yana da ‘yancin rayuwa da kuma gudanar da harkokinsa a ko ina a Najeriya ba tare da an hana sa ba ko kuma an yi masa wani iyaka ba.
Ina da yakinin cewa ‘yan Najeriya da yawa na da irin wannan tunani fa fahimci.
Sai dai hakan ba yana nufin cewa babu wasu muhimman ababe da ke ci mana two a kwarya bane.
Kowane bangare yana da korafinsa. Amma dadin tsarin da ake tafiyar da kasar a ka yanzu shi ne, yadda ya tanadin hanyoyin da duk wadanda suke ganin an yi musu ba daidai ba, za su iya gabatar da korafinsu da kuma yadda za a ci gaba da tafiya tare.
Majalisar dokoki ta kasa da kuma majalisar koli ta kasa su ne wuraren da doka ta yarda a tattauna manyan batutuwan da suka shafi Najeriya.
Baki ya zo daya a kasa baki daya cewa ya fi kamata a ci gaba da zama tare maimakon a raba kasar.
Bugu da kari, ina kira da rundunonin tsaro da kada nasarar da aka samun a watanni 18 da suka gabata ta sa su, su rage kaimi.
Wajibi ne mu yaki ‘yan ta’adda da miyagu kuma mu ga bayansu saboda mu ci gaba da rayuwa cikin zaman lafiya da tsaro.
Wannan ya sa za mu kara kaimi ba kawai a yaki da ‘yan Boko Haram ba wadanda suka fito da sabbin hanyoyin kai wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba hari.
Hakazalika za mu sa kaimi a yaki da masu satar mutane don neman kudin fansa da rikicin Fulani makiyaya da manoma da rikicin kabilanci wanda wasu ‘yan siyasa masu munanan manufa suke rura wutarsa. Za mu magance su duka.
A karshe ‘yan uwana ‘yan Najeriya abin da ya dace yanzu shi ne mu manta da bambance-bambancen da ke tsakaninmu, mu fuskanci wadannan kalubalen da suka shafe mu duka; wato gyara tattalin arziki da bunkasar siyasa da hadin kan kasa, har ila yau, da samar wa ‘yan Najeriya zaman lafiya mai dorewa.
A shirye nake don ganin mun cimma wannan burin da kuma ganin dorewarsu. Ina farin cikin dawowa gida sosai.
Na gode kuma Allah Ya albarkaci kasarmu Najeriya.