Jami’o’in Ilorin da Zaria aka fi rububin shiga

0

Wani binciken kwafaf da aka gudanar ta hanya na’ura mai kwakwalwa, ya tabbatar da cewa a shekarar 2017, an fi rububin shiga Jami’ar Ilorin da ke jihar Kwara.

Rahoton ya ce mai bi mata wajen zumidin shiga ita ce Jami’ar Ahmadu Bello, da ke Zaria. An tantance wannan kididdiga ne daga jami’o’I 148 wadanda gwamnatin tarayya ta amince da su a kasar nan.

Rahoton dai na hadin na hadin guiwa ne tsakanin Mujallar Intelligence da kuma Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a, JAMB. An yi la’akari ne jami’ar farko wacce dalibai ke fara zabe a matsayin wadda su ka fi kaunar shiga.

Cikin 2017, dalibai 104,038 ne su ka cika fam na neman shiga jami’ar Ilorin a matsayin ita ce zabin su ta farko.

Wannan adadi ya kunshi kashi 10 daga cikin 100 na sauran jami’o’in kasar nan har 40. Ko a shekarar da ta gabata, Jami’ar Ilorin ce aka fi rububin neman shiga, inda dalibai 103238.

Jami’ar Ahmadu Bello wadda ta zo ta biyu, an samu dalibai da su ka cikac fam na rububin shigar ta har guda 89,688.

Sauran Jami’o’in da su ka biyo baya sun hada da Jami’ar Benin, Jami’ar Nsukka, Lagos, Jami’ar Bayero wadda ta zo ta shida da dalibai 68,241 wadanda su ka yi rububin neman shigar ta cikin 2017.

Jami’ar Dutsinma, Gashua ta Jihar Yobe da Budaddiyar Jami’a su ne su ka zo karshe da dalibai 3807, sai 1897 da kuma 110.

Share.

game da Author