Dubban Daliban Najeriya ne suke tururuwa zuwa Jami’ar Maryam Abacha da ke Maradi Kasar Nijar.
Jami’ar na karantar da digiri a fannoni daban-daban da ya hada da na Kula da lafiyar jama’a aikin asibiti, da sauransu.
Jami’ar wanda shekaranta uku Kenan da kafuwa ta yi rawar gani wajen yaye dalibai da suka sami kwarewa a fannonin kimiyya da aikin asibiti wato Nursing.
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aliyu Wammako, wanda shine ‘Pro-Chancellor’ Jami’ar ya ce daya daga cikin makasudin kafa jami’ar a kasar Nijar shine don a kara karfafa dankon zumunci tsakanin kasahen Nijar da Najeriya.
Bayan haka kuma Jam’iar ta samu karbuwar da su kansu mahukuntan makarantar basu dauka haka ba a cikin dan kankanin lokaci da kafa ta ba.
Yan Najeriya da wadansu yan kasashen Afrika ne suke karatu a Makarantar.
A bikin yaye daliban ta na farko da jami’ar tayi a watan da ya gabata, Dalibai sama da dari uku ne suka kamala karatunsu a jami’ar.
Dayawa daga cikinsu sun nuna gamsuwarsu da irin karatun da suka samu a jami’ar.
Da yake jawabi a wajen bukin Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje wanda yana dag cikin manyan baki y ace kafa wannan jami’a da akayi a kasar Nijar yana da matukar amfani sosai ganin yadda ake kokarin ganin an samu hadinkai da ci gaban kasa a tsakanin kasashen biyu.
Shugaban Jami’ar Adamu Gwarzo ya nuna farincikin sa ganin yadda jami’ar ta samu karbuwa cikin dan kankanin lokaci.
” Wannan Jami’a mun kirkirota ne domin mutanen kasashen mu biyu ad kuma don ci gaban ilimi a kasashen. Yanzu mun samu karbuwa sosai inda gashi har Allah yayi yau muna yaye daliban mu na farko.”
Ya ce nan gaba kadan za su fara wasu kwasa kwasai da ya hada da kimiyar yanar gizo da shirya fina-finai.