Illolin jinkirta fitsari a jikin mutum

0

Sau da yawa mutane kan hana kansu yi fitsari saboda rashin bandaki musamman idan ban daki bashi da tsafta ko kuma na ganin dama zuwa wani lokaci.

Hakan yakan sa akamu da wasu matsaloli da ya shafi lafiyar jikin mutum.

Wata likitan mata mai suna Miriam Oreouwa ta ce duk da cewa hana kai yin fitsari a bandakin da bashi da tsafta na da mahimmancin gaske don yakan sa a kubuta daga kamuwa da cutar da akan kama a irin wadannan wurare.

Illolin hakan sun hada da:

1. Yawan hana kai yin fitsari a lokacin da ya kamata na kawo cutar koda da ake kira ‘Kidney stone’ da turanci.

2. Yana kawo rashin karfin bangaren jikin da ke hana fitsari fita a kowani lokaci wanda ake kira da ‘Pelvic Floor’.
Saboda hakan ne likitan ta shawarci mata da su daina yawan rike fitsari a marar su domin haihuwa na iya kawo musu wannan matsalar.

3. Rashin yin fitsari a lokacin da ya kamata na sa mutum jin zafi a mararsa wanda hakan ke iya daukar tsawon lokaci ana fama dashi.

4. Yana kawo cuwon ciki.

5. Yana kawo ciwon mara da jin zafi a mara a lokacin da ake yin fitsari.

Share.

game da Author