Hanyoyi 5 da zai taimaka wajen gyara fannin kiwon lafiya a Najeriya

0

1. Gwamnatin tarayya ta kadamar da dokan kiwon lafiya wanda ake kira da ‘NHAct ‘ wanda zai taimaka wajen bayana hakin da ya rataya akan kowace sassan gwamnati musamman wand ya shafi kudi.

2. A gyara hanyoyin zuwa aibitocin da ke karkara da wanda ke zuwa biranen kasarnan don samun sauki wajen daukan marasa lafiya zuwa asibiti sannan idan cutar ta fi karfin asibiti za a iya aikawa da su asibitocin da ke birane.

3. Inganta hanyoyin samun bayanai akan aiyukkan kananan hukumomi da cibiyoyin kiwon lafiya musamman wadanda ke cikin karkara ta hanyar saka mutanen a shirye-shirye da akeyi domin su.

4. Kirkiro shirin da zai bada damar sa kowa a shirin inshorar kiwon lafiya na kasa.

5. Gwamnati ta mai da hankalinta sosai wajen bunkasa fannin kiwon lafiyar mutanen karkara.

Share.

game da Author