HAJJIN BANA: ’Yan Najeriya bakwai sun rasu rayukan su

0

Hukumar Alhazai ta kasa ta tabbatar da cewa yawan ‘yan Najeriya da suka mutu a Saudiyya ya kai mutane bakwai.

Shugaban Hukumar Abdullahi Mohammed ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke tattauna da ‘yan jarida a filin Arafat, yau Alhamis.

Tunda farko dama a ranar Talata, Mohammed ya shaida cewa an samu asarar rayuka biyar. Ya yi wannan jawabin ne tun a yayin zaman tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkokin aikin Hajji.

Duk da cewa har zuwa yanzu ba a bayyana sunayen mamatan ba, amma dai shugaban hukumar ya ce akwai daga Kogi, Kwara, Katsina da kuma Kaduna.

“Mun rasa mahajjata bakwai, wadanda dukkan su mutuwa ce ta ciwon ajali da karar kwana, ba hadari su ka yi ba. A cikin su akwai maza da kuma mata.”

“Sai dai mu kara godiya ga Allah, domin idan mu ka duba za mu ga yawan asarar rayuka a wannan shekarar, bai kai na shekaru goma zuwa 15 da suka gabata ba.”

“Ina kuma so na sanar da ku cewa mun fito da lambar waya domin a kira saboda neman agajin gaggawa a kowane lokaci, cikin awa 24. Duk wanda ya shiga cikin wani mawuyacin hali, to ya gaggauta kiran: 90008251 da kuma 920008251.

Ya kuma nuna gamsuwar sa da canjin da aka samu wajen saukake tafiya Arafat daga Mina, wanda ya ce a shekarun baya ana kwashe awoyi da yawa, amma yanzu cikin minti 15v zuwa 20 mahajjaci ya isa.

Aikin Arafat ya na daya daga cikin farillan aikin Hajji. Ba a dauke wa kowane mahajjaci zuwa Arafat ba. Ana tafiya Arafat ne daga Mina da safe. Ana so a fita daga filin Arafat kafin faduwar rana.

Daga nan za a koma Minna, amma kuma za a yada zango a filin Musdalifa akwana a sararin filin. Gaba dayan Alhazai duk mukamin ka a duniya, kowa a filin Allah zai kwanta, har bayan Sallar Asubahi. Ko da yake wasu na kwanciya a cikin kananan tantina masu kama da akulki.

Da safe ranar 10 Ga Zul-Hajji, ranar Babbar Sallah kenan, za a sake darzazawa ana tafiya domin zuwa jifar Shaidan ta farko. Kowa zai keta ya wuce ta Mina inda tantinan kwanan Alhazai su ke, ba a tsaya ba har sai an dangana da wurin jifa. Sai dai ana so Alhaji ya tsinci duwatsu bakwai da zai yi jifa da su, tun kafin ya isa wurin.

Duk wanda ya yi jifa, ba zai koma Mina cikin tantin sa ya huta ba, sai ya zarce ya koma cikin Makka, ya doshi Ka’aba domin yin Dawafi da kuma Safa da Marwa.

Daga can sai ya fice daga Ka’aba, ya yi aski, ya koma masaukin sa na cikin Makka ya yi wanka, ya ci abinci kuma ya huta. Sai ya cire harami ya sa kaya masu kyau, yamma na yi sai kuma ya koma Mina, inda zai kara yi kwanaki biyu a can, kullum safiya ya na zuwa ya na jifan Shaidan.

Daga nan aikin Hajji ya kare, saura ziyara Madina, ga wanda bai je tun farko kafin ya isa Makka ba.

Allah ya karbi ayyukan ibada, amin.

Share.

game da Author