HAJJIN BANA: ‘Yan Najeriya 5 sun rasa rayukansu a Makka

0

A yau Talata ne shugaban hukumar NAHCON Abdullahi Muhammed ya sanar da mutuwan wasu mahajjata hudu a Makka.

Ya fadi haka ne a taron da hukumar tayi na shirye-shiryen Hawa Arafat.

Duk da cewa bai fadi sanadiyyar rasuwar mutanen 4 ba ya ce hukumar tayi haka ne saboda wadannan bayanai ne na ‘yan uwan mamatan.

Ya kuma roki gidajen jaridu da kada su bayyana sunaye da abin da yayi sanadiyyar mutuwan mahajjatan.

Bayan haka hukumar NAHCON ta sami labarin mutuwan wani mahajjaci daga jihar Kwara.

Hukumar ta sami labarin hakan ne baya ta gama sanar da mutuwan mahajjata hudu da suka rasu a Makka.

Share.

game da Author