HAJJIN BANA: Mutane 400,000 aka hana shiga kasar Saudiyya saboda takardun karya

0

Jami’an tsaron kasar Saudiyya sun hana wasu mutane 400,000 da suka nemi shiga kasar ba tare da takardun izinin shiga kasar na ainihi ba.

Duk da cewa mutanen sun taho kasar ne domin yin aikin haji hukumar harkokin cikin gida na Saudi taki basu daman shiga kasar saboda takardun karya da kuma don samar da tsaro ga wadanda ke aikin Haji a kasar.

Ma’aikatan harkokin cikin gidan kasar ta sanar da cewa sama da baki miliyan 1.7 ne zasu yi aikin hajji a kasar bana inda ‘yan kasa 200,000 zasu yi.

Jami’an tsaro 100,000 ne kasar ta wakilta domin samar da tsaro ga mahajjata a duk inda suke a kasar.

Mansour Al-Turki, Kakakin ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ya ce kasar ta kakkabe wasu shirin hare-hare da aka nemi kaiwa garuruwan Makka da Madina cikin shekarun da suka wuce.

Ranar Alhamis ne Alhazai zasu hau arfa, sannan Juma’a kuma Babban sallah.

Share.

game da Author