Shugaban sashen kula da aiyukka na hukumar alhazai ta kasa, Abdullahi Modibbo ya ce zuwa yanzu sun kwashi maniyyata aikin hajjin bana 37,388 daga cikin 65,271 zuwa kasar Saudiyya.
Ya sanar da hakan ne da ya ke zantawa da manema labarai ranar Laraba a Abuja.
Ya ce za su kwashe sauran maniyyatan da suka rage 27,883 kafin ranar 26 ga watan Agusta wanda shine ranar karshe na jigilan maniyyatan ta aka tsayar.