HAJJIN BANA: Manoma ne suka fi yawa a wadanda suka tafi aikin haji bana daga Najeriya – Abdullahi

0

Shugaban hukumar NAHCON Abdullahi Muhammad ya jinjina wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan bunkasa aiyukkan noma da gwamnatinsa tayi a Najeriya ganin cewa kusan duka mahajjatan bana daga kasarnan manoma ne.

Abdullahi Mohammed ya ce a wannan shekaran maniyyatan da hukumar ta yi jigila zuwa kasa mai tsarki ta fi na kowace shekara yawa.

Ya ce sun yi jigilan maniyyata 81,200 wanda kashi 60 bisa 100 daga cikin su manoma ne da suka biya Naira miliyan 1.5 kudin kujeran hajji.

Daga karshe Abdullahi Mohammed ya yi alkawarin gyara aiyukkan hukumar NAHCON don samar da ingantacciyar kula ga mahajjata.

Share.

game da Author