Hajjin Bana: Bamu da matsala wajen jigilar mahajjatan jihar Katsina – Abu Rimi

0

Shugaban hukumar kula da jin dadin mahajjata na jihar Katsina KSPWB Muhammad Abu Rimi ya ce wasu ‘yan adawa ne suka zuga mahajjatan jihar Katsina su gudanar da zanga-zanga saboda matsalar jinkirin da aka samu na daukan su zuwa kasar Saudiyya.

Jam’iyyar PDP wanda sune kan gaba wajen yadda wannan farfaganda da ya yi sanadiyyar hada wannan zanga-zangan sannan suka ce jinkirin ya nuna kasawar jam’iyyar APC ne karara a jihar.

Jam’iyyar PDP a jihar ta ce jinkirin ya wahalar da mahajjata wanda ya hada da kwana flin Allah ta’ala na jiragen sama.

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina Salisu Majigiri ya koka kan yadda jam’iyyar APC ta kasa shirya jigilar mahajjatan yadda ya kamata wanda hakan kamar yadda ta sanar kasawa ce daga jam’iyya mai ci a jihar, wato jam’iyyar APC.

A yanayin da ake ciki mahajjata 2,086 daga cikin 4,0000 sun sami tafiya zuwa kasar Saudi a jirgi na biyar da ta tashi a yau.

Share.

game da Author