Gwamnatin Tarayya za ta gyara tituna a jihohin Filato da Kwara

0

Ministan wutan lantarki da aiyukka Babatunde Fashola ya ce gwamnatin tarayya za ta gyara titunan jihohin Filato da Kwara da kudaden da ya kai Naira biliyan 20.6.

Ya fadi haka wa manema labarai bayan kammala taron majalisar zartaswa na tarayya FEC wanda mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta ranar Laraba.

Babatunde Fashola ya bayyana cewa sun amince su kashe Naira biliyan 10.4 wajen gyaran titin Pankshin-Balank-Yalen-Salak-Gindiri dake jihar Filato sannan za a kashe Naira biliyan 10.2 wajen yaran titin Sharre-Patigi dake jihar Kwara.

Bayan haka kuma Fashpola y ace gwamnati ta kamala tattaunawa da take yi da wata Kamfanin da zai samar da sabbin mitocin wutan lantarki da guda miliyan 3.

Share.

game da Author