Gwamnatin tarayya ta samar da biliyan 3 don gina makarantun yankin arewa maso gabas

0

Shugaban hukumar bada ilimi a matakin farko UBEC Hameed Bobboyi da ministan ilimi Adamu Adamu sun sanar da samar da kudade da gwamnatin tarayya ta ware don gina makarantun yankin arewa maso gabacin kasar.

sun ce gwamnatin tarayya ta yi haka ne ta karkashin hukumar UBEC.

Ya kara da cewa za a yi amfani da kudin domin taimaka wa mata da matasa wajen samun horo akan sana’o’in hannu.

Hameed Bobboyi yace nan da watan satumba hukumar za ta kirkiro da sabbin shirye-shirye don bunkasa fannin ilimi a yankin.

Daga karshe ya ce kudaden zai taimaka wajen kara wa yara da iyaye karfin guiwan zuwa makaranta domin samun Ilimi.

Share.

game da Author