Gwamnatin Tarayya ta nemi kotu ta soke belin Nnamdi Kanu

0

Gwamnatin Tarayya ta nemi kotu da soke belin dan taratsin neman kafa Biafra, Nnamdi Kanu.

Wata sanarwa da hadimin Ministan Shari’a, Abubakar Malami, mai suna Salihu Isah ya sa wa hannu, ta nuna dalilan hakan da su ka hada da kin bin umarnin kotun da ya yi ta hanyar karya dukkan sharuddan belin da aka gindaya masa.

Sanarwar wadda aka sa wa hannu a ranar Juma’a, ta kuma nemi kotun ta sa jami’an tsaro su kamo shi a kulle shi, har zuwa yadda shari’ar da ake yi masa za ta kaya.

Nnamdi Kanu tare da wasu da aka kama su tare, su na fuskantar tuhumar cin amanar kasa ne. An tsare su a kurkukun Kuje, da ke kusa da Abuja. Sai dai kuma an bada belin Kanu, wadancan kuma har yau su na tsare, duk da cewa su ma sun nemi a ba da belin su.

Wani babban jami’in tsaro ya shaida wa PREMIUM TIMES tun a jiya Alhamis cewa matsawar aka bada umarnin kama Kanu, to za su kamo shi ba tare da wani bata lokaci ba.

Share.

game da Author