Gwamnatin Tarayya ta fara gina gidaje 2,736 a kowace jiha a kasarnan

0

Ministan wutan lantarki, aiyukka da gidaje Babatunde Fashola ya sanar da aiyukkan ginin gidajen da ma’aikatarsa ta fara yi a jihohi 33 a fadin kasa Najeriya.

Ya ce gwamnatin tarayya za ta gina gidaje 2,736 a kowace jiha a fadin kasarnan.

Ya kara da cewa sanadiyyar aiyukkan ginin da suke yi mutane da dama a kasar sun sami aikin yi. Ya ce ma’aikatar ta dauki ‘yan kwangila 653 sannan ma’aikata 54,680 sun sami ayyukan yi daban daban.

Bayan haka ya yi kira ga Mutane da su daina yawan korafi da jejjefa maganganu batanci ga gwamnati saboda basukan da ta karbo domin aiwatar da wasu aiyyuka. Ya ce basuka ne da gwamnati ke bukata kuma tuni ta fara biyan biyansu ma.

Share.

game da Author