Gwamnatin Jihar Kano ta bada kyautar motar kirar bas mai daukar fasinja 18 ga Kungiyar Kwallon Nakasassu, mai suna Kano Pillars Para Soccer.
Gwamnan Jihar Abdullahi Ganduje ne ya bayyana haka. Ya na mai cewa an yi musu kyautar ne domin a kara zaburar da su, duk kuwa da cewa akwai matsalolin da ke tattare da su, hakan bai sa an maida su na-ware-ga-dangi ba.
Gwamnan ya kara da cewa hakan kuma zai kara musu kwarin guiwa, ganin cewa su ne su ka yi nasarar cin kofin kalubale na Ranar Kawar da Cutar Polio ta Duniya, da Nijeriya ke shiryawa. Kungiyar dai ta yi nasarar lashe gasar ta kasa har sau biyar, inji gwamnan.
Ya kuma sha alwashin ci gaba da tallafa musu domin su samu nasarar shiga gasa gami da yin nasara a kowace gasar wasannin kwallon nakasassu da za shirya nan gaba.
Da yake sharhi dangane da wasan karshe na cin Kofin Kwallon Nakasassu na Gwamna Ganduje, ya ce kungiyoyin biyu da su ka kafsa, na Fagge da Nassarwa sun burge shi sosai.
An tashi wasan da ci 4-2, inda gwamnan ya daba kyautar kofi da kudi naira dubu dari biyar ga kungiar karamar hukumar Fagge, wadda ta zo ta biyu, wato ta karamar hukumar Nassarawa, ta samu kyautar naira dubu dari hudu.
Kungiyoyi biyu da suka kai ga wasan kusa da na karshe kowacen su ta samu kyautar naira dubu dari biyu da hamsin.