Gwamnatin jihar Kaduna ta bada kwangilar samar da kujeru 256,182 domin makarantun gwamnatin dake jihar.
Ma’aikatar ilimi,kimiya da fasaha ta sanar da haka sannan ta kara da cewa shirin kula da bada ilimi na gaggawa (Education Emergency Intervention Programme) ta dauki nauyin samar da kujeru 186,182.
Ma’aikatar ilimi ta bayyana cewa makarantun firamare za su sami 167,982 daga cikin kujerun sannan makarantun sakandare za su sami 18,200.
Ma’aikatar ta kuma ce a yanzu hakan ta bada kwangilar karo wasu kujerun da suka kai 70,000 wanda jimillar hakan ya kai 256,182.
Kwamishinan ilimi na jihar Andrew Nok ya ce gwamnatin ta fara raba kujeru 90,000 ga wasu makarantun.
Ya fadi hakan ne a lokacin da ya ke bada kujeru 700 wa makarantan sakandaren dake Sabon Tasha.