Gwamnati ta kwace lasisin wasu Asibitoci a jihar Nasarawa

0

Gwamnatin jihar Nasarawa ta rufe wasu cibiyoyin kiwon lafiya da shagunan magani 42 da suke aiki ba tare da lasisin yin haka ba.

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Nasarawa Daniel Iya ne ya sanar da haka a garin Lafiya.

Ya ce sun yi haka ne domin su kawar da baragurbin asibitoci da wuraren gwajin da ke neman ya zama ruwan dare a jihar.

Ya kuma ce jihar ta kafa dokar cewa daga yanzu kafin a bude wani asibiti ko wurin gwaji sai an sami cikaken izinin daga ma’aikatan kiwon lafiya na jihar.

Share.

game da Author