Gwamnatin tarayya ta bada tallafin shinkafa da ya kai tan 5,000 wa shirin kula da masu fama da yunwa na majalisar dinkin duniya WFP domin raba wa mazauna sansanonin da ke yankin arewa maso gabacin kasarnan.
Shirin WFP ta sanar da haka ne ranar Alhamis inda ta kara da cewa gudunmawar zai taimaka wajen ciyar da mutane rabin miliyan na mazauna sansanonin musamman wadanda ke fama da yunwa a jihohin Adamawa, Borno da Yobe.
‘‘Mun karbi kaso na farko na buhunan shinkafan sannan muna jiran gero tan 2000 wanda gwamnatin Najeriya ta yi alkawarin ba mu’’.
Bayan haka shirin WFP ta ce yawan gudunmawar da suka samu ya basu damar shawo kan matsalar rashin iya ciyar da mutane da ya kai miliyan daya amma yanzu suna neman abincin da za su ciyar da mutane 1.36 saboda lokacin damina da ake ciki.
Daga karshe shirin WFP ta ce banda gudanmawar dala 100 da gwamnatin Amurka ta bayar ta dauki nauyin biyan kudin dakon buhunan shinkafan da za a rarraba a jihohin Adamawa,Yobe da Borno.