Wasu mazauna garin Legas sun gudanar da zanga-zanga kan yadda fyade ke neman zama ruwan dare a jihar da kasa baki daya.
Masu zanga zangar sun yi tattaki zuwa ofishin gwamnan jihar Legas don nuna fushinsu da mika kukansu ga gwamnan game da yadda fyade yak e neman ya zamo ruwan dare a jihar.
Daya daga cikin ‘yan zanga-zangan mai suna Laila ta fadi wa gidan jaridar PREMIUM TIMES cewa ya kamata gwamanti ta dauki matakai wajen magance wannan matsala kafin mutane su fara daukan fansa da kansu.
Ta kara da cewa wasu sun ce yadda mata ke sanya tufafin da ke nuna tsiraicinsu ne ya sa ake yi musu fiyade amma ta yaya yara kanana ke sanya kayan da har za kaga su ne ma suka fi fadawa tarkon wadannan mutane musu aikata fyade din.
A jihar Gombe ma wata sun gudanar da irin wannan zanga-zanga.
Wata jami’ar kungiya mai zaman kanta ‘Women Situation Room’Jamila Sulaiman ta ce sun sanya bakaken kayane ne don su nuna bakin cikin su kan yadda ake yi wa ya’yan su fyade babu kakkautawa a jihar.
Bayan haka Kungiyar kare hakin Musulmai MURIC ta ce mutanen da suka gudanar da zanga-zangan sun bata lokacin su ne kawai musamman mutanen da suka je ofishin gwamnan jihar Legas.
Yace yanzu mata iyaye ne da kansu ke saya wa ya’yansu irin kayan da zai nuna tsiraicinsu wanda hakan kan tunzura wasu mazan da ba su da karfin Imani a zukatansu yin hakan.
Ya yi kira ga iyaye da su kula da tarbiyyan ya’yan su tun daga gidajensu.
Discussion about this post