Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya musanta maganganun da ake yadawa cewa ya yi rantsuwa idan har Buhari ya dawo Najeriya da ran sa, to shi zai kashe kan sa.
Ya ce hakan karya ce aka kitsa masa.
Kakakin yada labaran gwamnan, Idowu Adelusi, ya shaida wa PREMIUM TIMES a ranar Litinin cewa wannan zance “duk sharrin ‘yan jam’iyyar APC ne a jihar sa.
“Fayose bai taba fadar wannan magana ba, cewa wai idan Shugaban Kasa ya dawo da ran sa shi zai kashe kan sa. Karya ce kawai”
Ya ce gwamnan ya na yi wa shugaban kasa fatan alheri, kuma ya na yi masa kyakkyawar addu’a kamar yadda saura ke yi masa.
Idan ba a manta ba, an sha ruwaito irin wadannan labarai da ake dangantawa da Fayose. A ranar 22 Ga Yuli ne dai aka ruwaito Fayose na cewa zai kashe kan sa muddin Buhari ya dawo da ran sa.
Ya sha nuna cewa Buhari ya na Landan mutu-kwakwai-rai-kwakwai. Na baya-bayan nan shi ne kalamin da ya rika yi cewa ya na da hotuna 11 da ya yi barazanar watsawa duniya ta gani, cewa Buhari bai san inda ya ke ba, ya koma kamar kwarangwal.
Farkon watan Fabrairu ne dai cikin 2015, kusa ga zaben shugaban kasa Fayose ya dauki nauyin buga wata talla a cikin manyan jariddun kasar nan, inda ya ke jan hankalin Najeirya da kada zabi Buhari, domin a cewar sa, sun gaji da rufe gawar shugabannin kasa a lokacin da su ke kan mulki.
Discussion about this post