Tambaya: Malam ayi min bayani kan falalar kwanaki goman wata dhul-hijjah
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Falalar Allah ta na da yawa ga bayinsa, sabo da haka ne ya samarwa bayinsa lokuta na musamman don yawaita ambatonsa, da ayyukan kwarai, suna rige-rige a cikinsu, suna neman kusanci zuwa ga ubangijin su.
Kwanaki goma na Dhul-Hijja suna daga cikin mafi girman daraja a cikin lokuta na muasamman. Kuma Annabi Muhammad (SAW) ya tabbatar da cewa sun fi sauran kwanakin duniya girman daraja.
Babu wani aikin ibada da yafi girman daraja fiye da a cikin wadannan kwanaki goma na Dhul-Hijja. Kenan bawa zai jajirce don yawaita ayyukan alhairi don
ribatan wannan kwanaki goma.
Ayyukan Ibada da Bawa zai yi a cikin kwanaki Goman Dhul-Hijja
Lallai ne bawa ya fuskanci wadannan kwanaki da ikhlasi a cikin ibadunsa, kuma yayi kwadayin raya kwanakin da ayyukan alhairi kamar haka:
1 – Tuba: Duk musulmi ya tuba ga Allah tuba na gaskiya, Allah ya ce : ku tuba ga Allah baki daya ya ku muminai lallai za ku ci nasara. (Nur:31)
2 – Nisantar Zunubai: Bawa ya nisanci sabon Allah, sabon Allah da zunubi suna nisartar da bawa daga rahamar Allah da yafiyar sa. Kuma Allah yana kuntatawa bayi sakamakon zunubai.
3 – Zikiri: kamar kabarbari, tahmidi da hailala, da sauran dukkanin ambaton Allah.
4 – Karatun Al-kura’ni.
5 – Biyayya ga iyaye, shugabanni, da malamai da sauran nagaba.
6 – Sulhu tsakanin mutanen da suke da sabani ko gaba.
7 – Kyautatawa marayu, makwabta, ‘yan-uwa da sauran al’umma.
8 – Ciyarwa da biyan bukatun talakawa da masu rauni.
9 – Ziyarar marasa lafiya.
10 – Azumi
11 – Sallah.
12 – Sadaqah.
13 – Layya.
14 – Hajji da Umra.
15 – Addu’a.
16 – Sada zumunta da sauran dukkanin ibadu.
FALALAR KWANAKI GOMA NA DHUL-HIJJA
1) Allah ya yi rantsuwa da kwanaki goman Dhul-Hijja a cikin suratul fajari sura ta 89 aya ta 1-2.
2) Sune kwanakin da ake kira “AYYAMIN MA’ALUMAT” (kwanaki sanannu) : Allah yayi umurni ga muminai da su ambace sa a cikin kwanaki sanannu (Al-Haj: 28).
3) Sune kwanaki mafi girman daraja a cikin kwanakin duniya.
4) Ana ninka ladan aiki na kwarai ninkin-ba-ninkin a cikin kwanaki goman Dhul-Hajji.
5) Ana amsa addu’o’in bayin Allah a cikin kwanaki goman Dhul-Hajji.
6) Ana kankare zunubai a cikin kwanaki goman Dhul-Hajji.
7) Ana ‘yanta mutane daga shiga wuta a cikin kwanaki goman Dhul-Hajji.
8) A cikinsu ake da ranar arafa, wanda ake kira YAWMUL HAJJUL AKBAR wato ranar hajji mafi girma, kuma ranar gafara da ‘yanci daga wuta.
Kuma arafa itace hajji inji manzon tsira (SAW).
9) A cikinsu ake da ranar Sallah Babba, rana mafi girman daraja a ranakun duniya.
10)A cikin kwanaki goman Dhul-Hajji ne shedan yake tuzarta, ya kunyata kuma ya wulakanta, a lokacin da zai ga tarin mutanen da Allah yake ‘yantawa daga shiga wuta.
11) Girman darajar kwanaki goman Dhul-Hajji baya misaltuwa, domin kwanakin sun kunshi mafi girman ibadu a cikin addinin musulunci, kamar Sallah, Azumi, Sadaqah, Hajji, Umra da yanka. Babu wasu kwanaki da suka hada duk wadannan ibadu baki daya a cikin su.
FALALAR AIKIN IBADA A CIKIN KWANAKI GOMA NA DHUL-HIJJA
An karbo daga Ibni Abbas, Annabi Muhammad (SAW) ya ce: babu wasu kwanaki da aiki na kwarai ya fi soyowa ga Allah fiyi da kwanaki goman Dhul-Hajj. Sai sahabai suka tambaye shi, ya annabin Allah: shin koda jihadi don daukaka addinin Allah ne? sai annabi SAW yace: koda jihadi ne, sai dai mutumin da ya fita jihadin da rayuwarsa tare da dukiyarsa kuma bai dawo da komai ba.
Wannan hadisi ya nuna cewa ayyukan ibada a wadannan kwanaki sunfi girman falala, da daraja da lada fiye da mai jihadin da bai samu shahada ba. Kuma Allah ya fi son ayukan alhairi a cikin kwanakin fiye da kwanakin da ba su ba.
Allah ka bamu ikon bauta maka kamar yadda kake so, kuma ka karbi ibadunmu. Amin.
Imam Muhammad Bello Mai-Iyali – Harkatul Falahil Islam, Barnawa Kaduna.