Etsu Nupe ya nada Sani Danja Zakin Matasan Arewa

0

Etsu Nupe Mai martaba Yahaya Abubakarya nada Sani Danja dan farfajiyyar fina-finan Hausa ‘Zakin Arewa’.

Daruruwan abokai da yan uwane suka halarci taron nadin Zakin Arewan wato Sani Danja da aka yi a garin Bida jihar Neja ranar 5 ga watan Agusta.

Daya daga cikin masoyarsa na gani kasheni Aisha Yusufu ta ce wannan sarauta da aka ba Sani Danja ya zo a daidai domin jarumi ne mai tausayi da son taimakon Talakawa da matasa.

” Sani ya cancanci wannan karramawa musamman ganin yadda a kullum kara samun daukaka ya keyi. Gashi kuma yana tare da matasa a kullum.” Aisha tace.

Share.

game da Author