Eid-El-Kabir: Kada ka ci bashi don yin Layya – Mal Yusuf

1

Wani babban malami a jami’ar Ilorin, jihar Kwara Badmus Yusuf ya yi kira ga musulmai da su guji karbar bashi don siyan ragon layya.

Badmus ya yi wannan kira ne da yake jawabi a wani taro na musulunci a garin Ilori.

Ya ce musulunci addini ne mai sauki da babu tilastawa a cikinta saboda haka kowa ya yi abin da zai iya ba tare da dora wa kai abinda ba zai iya dauka ba.

” Niyya kawai ya isa amma cin bashi don yin layya bai dace ba. Saboda kawai don mutum yana son yayi layya sai ya ci bashi da kila ya zama mishi matsala bayan haka ba daidai bane.” cewar Badmus Yusuf na jami’ar Ilori.

Wannan malami yayi wannan Kira me tun a shekarar 2017.

A 2021, za a yi babban Sallah ranar Talata ne 20 ga watan Yuli.

Sai dai kuma bincike da wakilin mu yayi a Kaduna game da dabbobi, sun yi matukar tsahin gwauron zabi.

Ragon da aka siyar a bara naira 20,000, ya kai naira 40,000 a bana.

Share.

game da Author