EID-El-KABIR: Hukumar FRSC ta aika jami’anta 33,000 titunan Najeriya

0

Hukumar kare haddura ta kasa FRSC za ta aika da ma’aikatanta 33,000 a fadin kasan domin rage haddura a hanyoyin kasar musamman yanzu da ake shirin hidimar sallan layya.

Shugaban hukumar FRSC Boboye Oyeyemi ya ce ma’aikatan za su sa ido ne musamman ga wadanda ke karya dokar hanya da suka hada da, tukin ganganci, amfani da wayar lokacin da ake tuki da yin gudun da bai kamata ba.

Shugaban wayar da kan mutanen akan amfani da hanya na hukumar Bisi Kazeem yace ma’aikatan za su fara aiki ne daga ranar 31 ga watan Agusta zuwa 6 ga watan satumba sannan hukumar ta samar wa ma’aikatan isassun ababen hawa da motocin daukan mutanen da suka sami hadari zuwa asibiti.

Ya kuma yi kira ga mutane da su ba ma’aikatan hadin kai sannan ya bada lambobin waya kamar haka 070022553772 wanda za a iya kiran su da shi koda an sami wata matsala.

Share.

game da Author