Daminar Bana: Sallar rokon ruwa cikin watan Ogas a Katsina

0

Duk da ruwan sama kamar da bakin kwarya da zabgawa a fadin duniyar nan, har ta kai ga ambaliya a wasu garuruwa a kasar nan, a Jihar Katsina ana ci gaba da Sallar rokon ruwa a wasu yankuna.

PREMIUM TIMES HAUSA na da tabbacin cewa wasu yankuna na Kananan Hukumomin Mani, Dutsi da Ingawa na fama da karancin ruwan sama, har abin ya kai su ga wasu kauyuka ana Sallar rokon ruwa.

Ganau ba jiyau ba, ya shaida wa wakokin mu cewa, a ranar Talatar da ta gabata, ya je Karamar Hukumar Dutsi, inda a wani gari mai suna Dan’aunai ya iske wasu gungun mutane su na rokon ruwa.

“A bayan garin Dan’aunai mu ka hangi wasu gungun jama’a zaune su na karanta Alqur’ani. Kai da ganin irin haka ka san rokon ruwa su ke yi. To da mu ka matsa gaba, sai mu ka tambayi wasu masu wucewa, inda su ka tabbatar mana cewa ai rokon ruwa gungun mutanen da mu ka hanga a zazzaune su ke yi.”

Wannan ganau, ya kara shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa, da ganin yanayin yadda kasa ta bushe a Dan’aunai da kewaye, kai ka san ana bukatar ruwan sama sosai.

“Dawa ta yi kunshi, akasari ba ta fidda kai ba, to kuma ga shi ruwan sama ya yi karanci. Wannan kuwa a gaskiya ba karamin tashin hankali ba ne mai gona ya ga amfanin gonar sa ya na yaushi.”

Wani ganau din kuma ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ai ko cikin tsakiyar watan Agustan nan, yayin da ake shafe kwanki biyu ana sheka ruwa a wasu garuruwa, ya ce da idon sa ya ga inda ake rokon ruwa a cikin Karamar Hukumar Mani.

“Na je wani kauye mai suna Gargai inda na ga ana rokon ruwa. Dama kuma a wani garin ma na ga ana yi, amma ba zan iya tuna sunan sa ba.”

Majiyar mu ta kara da cewa ba abin mamaki ba ne a ga ana Sallar rokon ruwa a wasu garuruwan Katsina, musammam a cikin marka-markar watan Agusta. Tunda wasu yankunan sun kusanci iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Share.

game da Author