Ban yi mamaki ko kadan da labarin berayen da aka ce sun yi barna a ofishin Shugaba Muhammadu Buhari a lokacin da ya yi dogon hutu na kwanaki 103 a Landan ba. Duk wata katafariyar fada a duniyar nan, muddin aka ce a cikin dokar jeji ko a tsaunuka aka gina ta, to ba ka iya raba ta da wadannan beraye, kai har ma da macizai.
Shugabannin Amerika biyu, Jimmy Carter da George Bush duk sun sha fama da beraye a ofishin su, a cikin fadar da ake ganin babu wadda ta kai ta matakn tsaro a duniya. Akwai lokacin da ofishin Jimmy Carter ya shafe kusan watanni biyu ya na wari, saboda beraye sun mutu a cikin sili. Shi da kan sa ya fadi haka a cikin wani littafin tarihin sa da ya rubuta bayan ya kammala wa’adin sa.
A cikin littafin, akwai inda ya ce: “Wata rana mu na ganawa da Shugaban Kasar China, sai kawai mu ka rika jin warin mushen bera a cikin silin din ofishi ma. An sha wahala kafin a shawo kan labarin, har sai da wata rana na yi barazanar zan kori wasu.”
Wata rana matar George Bush na farko wato Barbara Bush, ta na wanka a kandami (swimming pool) a fadar White House kawai sai wani narkeken bera ta fito a guje, ya yi batan hanya, ya afka cikin kandamin da ta ke wanka.
An ce da ya ke akwai karnukan ta a kusa, nan take wani kare ya yi tsalle ya tinjuma ruwa, ya cafko beran, ya lamushe.
Shi ma tsohon Shugaban Amurka Barrack Obama akwai lokacin da ya sha fama da kyankyasai, har sai da zaman ofis din ya gagare shi. Duk wadannan bayanai su na nan cike da jaridu, ba boyayyu ba ne.
Idan mu ka dawo nan Abuja, ya kamata dukkan masu karatu ku sani cewa duk abin da aka ce an gani a cikin Villa, wallahi ba abin mamaki ba ne saboda wasu hujjoji da zan bayyana a yanzu, ba na siyasa ko adawa ba.
1. Fadar Shgaban Kasa a cikin surkukin jeji ta ke, kewaye a manyan bishiyoyi da kananan kwauren itace da manya da tsaunuka dogaye da kananan duwatsu.
2. Dukkan titunan cikin Fadar manyan bishiyoyi ne a hagun su da bayan su.
3. An sha bada labarin ana ganin macizai da sauran kananan namun daji a ciki.
4. Gaba dayan unguwar kan ta a cikin tsauni ta ke. Ka da ku manta, Kakakin Yada Labaran Goodluck Jonathan ya yi wani rubutu a cikin watannin baya, inda ya nuna cewa ana ganin aljanu manyan macizai da kuma jin muryoyi masu firgitarwa a cikin dare, duk a fadar Aso Rock Villa. Ya ce wasu jami’an tsaro sun sha ganin fatalwa da kambultu.
Kun tuna har cewa ya yi akwai wanda ya ce ya na ganin wasu mutanen ba a daidai su ke tafiya ba, sad-da-kai su ke tafiya, wato kafafu a sama hannaye a kasa?
5. Wasu bangarorin cikin Villa ko Dajin Falgore bai kai su surkukin jeji da tsaunuka ba. Duk wanda ke Abuja ya san wannan.
6. Ba na jin jami’an tsaro za su rika bari wani na shiga Ofishin Shugaban Kasa, musammam ganin yadda aka rika watsa rudun cewa wai asiri aka yi masa. Kenan ina da fahimtar cewa ofis din ya kasance a kulle.
7. Ita kan ta Abuja har yau har gobe a cikin jeji da manyan tsaunuka ta ke. Allah kadai ya san yawan tafiya da burgun da masu gadi ke kamawa a tsakar dare a cikin Abuja idan masu gida na barci.
8. Har yau a cikin tsakiyar Abuja ana ganin tsuntsayen jeji irin su cilkowa, makwarwa, mujiya, dubban jemagu, kurciya, balbela, kyari-kyari, hankaka da sauran wadanda mu a Arewa sai ‘yan farauta ke iya kamo su a cikin jeji, saboda ba mu ganin su kusa da mu.
9. Na yi shekara hudu a wani gida kusa da hedikwatar NTA, kusa da International Conference Center, Abuja. Sau da yawa na kan rika leka taga ina kallon kananan kadoji da tsari da kunkuru idan sun fito su na kiwo a bayan gidan mu, da ya ke akwai babbar magudanar ruwa wacce ta bi ta bayan gidan ta wuce har bayan CBN. Gidan ba ya da nisa da gidan Aminu Dabo a Abuja.
10. Na yi muku jam’u, bance kowane gida 100℅ ba. Amma wallahi na rantse a cikin ko wadanne gidaje 100, da wuya a samu gida 5 wadanda babu tsaka a cikin su. Har gidan Gwamnoni, Ministoci, Sanatoci da kowa ma. Abin da na san babu a Abuja, shi ne kuda, babu shi sosai saboda tsaftace garin da ake yi.
11. Abuja fa jeji ce. Bishiyoyin dorawa gandama-gandama da ke cikin Abuja ba su kirguwa sai an hada da malaman sansan. Ko ba ku san akwai kargo da baure da rimi da cediya da marke ba ne? Duk wadannan bishiyon da na lissafa ba fa shuka su aka yi ba, a nan suke, aka gina garin a inda su ke.
12. Ban ga dalilin da zan fito ina sukar Malam Garba Shehu ba. Idan kusanci ne, ya fi ni ga Buhari da ita fadar kan ta. Sannan kuma na san shi kakaki ne, ba ya busa kan sa, sai an busa shi, sannan za a ji amon irin busar da aka yi masa.
13. A yanzu haka gidan da na ke a tsakiyar jama’a ne. Ba ni da nisa ma da yada daga cikin ofishin jakadancin daya daga cikin kasashen Asiya da ke kusa da China. Amma kusan tsuntsaye na tayar da ni daga barcin safe, idan ma na makara. Kuma wasu tsuntsaye ban ma taba ganin irin su a dajin kauyen mu ba.
Kun ma san wani abu kuwa? Tsuntsayen a kan bishiyoyin gidan mu su ke rayuwar. A nan su ke sheka, su yi kwai, kuma su kyankyashe.
Ko yanzu da na ke rubutun nan da sanyin safiya, ina jin kukan marai da moli-moli har da kyari-kyara a cikin gidan mu. Idan zan fita kuma ta gefen su zan bi na tafi ofis. Su na kan bishiyoyi. Wadanda ba su amince da na bi kusa da su ba kuwa, sai su yi firrrr su tashi sama.
Kun sa ma na tuna wani baiti a wakar marigayi Musa Dankwaro Maradun a cikin wakar “Gagarau Mai Jiran Daga” wadda ya yi wa marigayi Alu ’Yandoton Tsafe:
“Da burgu da zoma da kurege,
Kowane na shi hali ya kai bamban,
Burgu shi ka rami cikin kunku,
Zomo shi ka kurhi gaton kalgo,
Na ga kurege ya yi bannag gaba,
Sai yai jawabi nai shi kau,
‘Na rega ka maigida’,
‘Kai wawa, in nish shiga ban hitowa nan’,
‘Ta inda dun nish shiga ban hitowa nan’,
Sai yay yi bula tai can daban,
‘In an rwakatan in hicewa ta.’”
To Allah ya sa idan an ritsa berayen a karkashe su, kada su fice ta baya, su afka wani ofishin, labari ya kara shan-bamban.
Discussion about this post