Ministan Harkokin Ma’adinai, Kayode Fayemi, ya zargi jami’an tsaro wajen daure wa ‘yan China gindi su na hakar ma’adinan kasar nan ba tare da izni ba, musamman a jihar Filato.
Fayemi ya yi wannan zargi ne yayin da ya ke wa jami’an tsaro jawabi a kauyen Kamfani Zurik, kusa da masarautar Bashar da ke Karamar Hukumar Wase, inda aka kama wasu masu hakar ma’adinai 20, cikin su har da ‘yan Chana su takwas.
An dai kama haramtattun mahakan ne a ranar Litinin din nan a bisa umarnin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara a kan Harkokin Tsaro, Ali Monguno.
“Abin takaici ne kwarai a ce wai jami’an tsaro ne ke bai wa masu hakar ma’adinai kariya. Idan ba haka ba, me ya sa jama’a ke gadin wurin? Inji Ministan a cikin fushi.
Wakilin PREMIUM TIMES ya lura da cewa akwai shingen jami’an tsaro musammam a kan rikicin Jos, STF har guda uku kafin a karasa wurin hakar ma’adinan.
“Wadannan fa duk haramtattun mahaka ma’adinai ne, kuma masu yi wa tattalin arzikin kasar nan zagon kasa ne.”
“Wannan tsiyar da su ke tabkawa ai ba za su iya yin haka ba a ko’ina cikin duniyar nan. Don haka mu ma a nan Nijeriya, ba za mu yarda da wannan aika-aika ba.” Haka Fayemi ya shaida wa jami’an tsaron.
Da ya ke jawabi, Gwamna Simon Lalong ya ce gwamnati za ta hukunta basaraken da ya bada izni ana kwasar arzikin kasar nan a yankin nasa.
Ya kuma sha alwashin za a canja wa DPO na karamar hukumar Wase wurin aiki.