Bana dai cinikin raguna ta sauka matuka musamman yanzu da al’umman musulmai ke shirye-shiryen hidimar sallar layya.
Gidan jaridan PREMIUM TIMES ta gudanar da bincike a kasuwanin raguna a jihar Kaduna kamar su ‘Yan Tumaki dake Kawo, kasuwar Zango dake Tudun –Wada da makamantan su inda ta sami bayanai akan yadda kasuwar take zuwa yanzu.
Masu siyar da raguna sun koka kan yadda mutanen basa zuwa siyyan ragunan kamar yadda aka saba yi a shekarun da suka gabata.
Kasimu Sani wanda ke sana’ar siyyar da raguna ya ce ‘‘A gasikiya bana babu cinikin raguna sosai kamar da. A bin mamaki shine mafi yawan ma’aikata sun karbi albashinsu amma babu wanda ya zo siyan rago. Mutane sun fi maida hankali wajen wadata iyalan su da abinci tukuna daga baya idan komai ya wadata sai a siya ragon.
Ya kara da cewa sun rage farashin ragunan bana ya ce karamin rago yanzu yakan fara daga Naira 20,000 ne zuwa sama.
Bayan haka mafi yawan mutanen da PREMIUM TIMES ta yi hira da su sunce bana da wuya rago ta yi tsada a kasuwani.
A ra’ayin Sanusi Danladi ma’aikacin gwamnati ya ce ‘’A yanzu dai girman rago ba shine damuwana ba domin layya ibada ce saboda hakan zan siya rago daidai yadda kudina suka ya kai ne.”
Wasu da aka tattauna dasu sun ce sun hada kudade su biyar domin siyan shanu siyi layyan da shi. Bayan haka wani magidanci ya ce ya riga da ya biya kosasshiyar bunsurunsa domin yin layya.
Yanzu dai ga dukkan alamu masu sana’ar siyar da rago sun shiga taitayinsu ne tun bayan kwantan da mafi yawansu sukayi a sallar bara.
Wana dan kasuwa a kasuwar dabbobi dake Zango, Tudun-Wada ya ce lallai kam bana fa da masu siyan da masu siyarwar suna taka-tsan-tsan ne wajen cinikin ragunan.
Ana sa ran za’ayi babban sallah ranar Juma’a mai 1 ga watan satumba 2017.