Cibiyar PTCIJ za ta horar da dalibai 200 a jami’oin kasar nan dabarun aikin Jarida

0

Cibiyar Binciken Labarai Da Bayanai ta Premium PTCIJ ta horar da daliban jami’o’in Najeriya kan dabarun bincike da yada labarai.

Cibiyar ta horar da daliban ne don samar wa kasa ‘yan jaridar da za su iya aikin zakulowa da yada labarai ta musamman da jama’a zasu iya dogaro dasu da nuna musu cewa sana’ar aikin jarida sana’a ce da zasu rike hannu bibbiyu don irin mahimmancin da take dashi.

PTCIJ

PTCIJ

Cibiyar ta fara gudanar da irin wannan horo ne a jami’ar Bayero dake jihar Kano sannan kuma ta fitar da wata Shafi a yanar gizo mai suna ‘Campus Reporter Website’ wanda zai taimaka wa daliba kimiyyar tsara labarai.

Cibiyar ta ziyarci jami’o’in a Najeriya da suka kai takwas wanda ya hada da jami’ar jihar Legas, jami’ar kimiya na jihar Neja,jami’ar Nnamdi Azikiwe dake Akwa (wanda ta kammala da daliban jami’ar ranar Asabar 30 ga watan yuli) dasauran su.

Cibiyar PTCIJ ta ce gidauniyar ‘Ford Foundation’ ne ta dauki nauyi koyar da dalibai 200 a Najeriya aikin Jarida.

PTCIJ

PTCIJ

Share.

game da Author