Cibiyar PTCIJ za ta gudanar da taro kan inganta kiwon lafiya a Najeriya

0

Cibiyar Binciken Labarai da Bayanai ta Premium Times, PTCIJ tare da kungiyoyi masu zaman kansu ‘Project for Advocacy in Child’ da ‘Family Health’, ‘PACFaH’ da ‘Project Pink Blue’ sun shirya taron domin tattaunawa akan matsalolin da fannin kiwon lafiya ke fama da su da hanyoyin da za a iya bi domin warwaresu.

Za a gudanar taron ne ranakun 24 zuwa 25 ga watan Agusta a cibiyar ‘Shehu Musa Yar Adu’a’ dake Abuja da karfe tara na safe.

Manyan bakin da za su halarci wannan taro sun hada da mai martaba sarkin jihar Kano Muhammadu Sanusi II wanda shine zai bada jawabi na musamman sauran sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ministan kiwon lafiya Isaac Adewole da masu ruwa da tsaki a harkar kiwon lafiya a duniya.

Cibiyar PTCIJ ta shirya taron ne don a samar da matakan da za su taimaka wajen samar da ingantacciyar kiwon lafiya mafi sauki wa mutanen kasa baki daya.

Share.

game da Author