Charly Boy ya sha da kyar a Kasuwar Wuse

0

Mawakinnan wanda aka fi sani da Charlie boy ya sha da kyar yau a Kasuwar Wuse da ke Abuja bayan hari da wasu matasa yan kasuwan suka kai masa.

Charly Boy ya zo Kasuwar ne tare da tawagarsa a ci gaba da zanga- Zangar da yake yi na kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka daga mulkin Najeriya.

Tun a makon da ya gabata ne mawakin ya fara wannan zanga-zanga a garin Abuja ya na kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka da mulkin Najeriya.

Ko da yake jami’an tsaro sun sha tarwatsa masu Zanga-zangar yau tare da tawagarsa sun shigo Kasuwar Wuse dake Abuja.

” Da kyar ya sha, domin matasa musamman yan Arewa sun nemi su lakada masa dan Karan duka sai Allah ya sa jami’an tsaro suka kawo masa dauki cikin gaggawa. Sai da aka yi ta harbin bindiga sama ana harba barkonun tsohuwa sannan matasan suka watse.” Inji wani dan Kasuwa

Daga baya, bayan jami’an tsaro sun dauke Charly Boy din sai suka dawo suka kwashe motocin da suka fito zanga-zangar da su.

images (3)

IMG-20170815-WA0002

Share.

game da Author