Hukumar shirya jarabawar kammala sakandare na kasashen yammacin Afrika WAEC ta ce ba za ta daga jarabawar da za a yin a ranar 4 ga watan Satumba ba duk da cewa ranar hutun Eid-el-Kabir ne a Najeriya.
Jami’in da ke kula da harka da jama’a na hukumar Demianus Ojijeogu ya sanar da haka a ranar Laraba da yake hira da gidan jaridar PREMIUM TIMES.
Ya ce hukumar ba za ta daga jarabawar 4 ga watan Satumba ba saboda hutun.
Gwamnatin tarayya ta ba da hutu ranar 1 da 4 ga watan Satumba.