Buhari ya yi tir da harin da aka kai coci

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi tir da harin da wasu yan bindiga suka kai coci da ke Ozubulu, jihar Anambara.

Kakakin fadar shugaban kasa Mal. Garba Shehu ne ya sanar da haka inda ya kara da cewa Buhari yayi mutukar nuna rashin jin dadinsa akai musamman ganin cewa wurin da aka kai wannan hari wuri ne na ibada.

Rundunan ‘yan sandar jihar Anambra sun sanar da mutuwan mutane 11 sanadiyyar.

Buhari ya tabbatar wa mutanen garin Ozubulu cewa gwamanti za ta ci gaba da mai da hankalinta wajen ganin ta samar da tsaro ga mutanen kasa baki daya.

Share.

game da Author