Gwamnonin jihohin Ribas Nyesome Wike, Abubakar Na Bauchi, Yari na Zamfara, Ganduje na Kano, Mataimakin gwamnan jihar Kaduna Barnabas Bantex na daga cikin jami’an gwamnati da suka tarbi shugaban kasa Muhammadu Buhari a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja.
Buhari ya sauka a filin jirgin saman da karfe 4:26 na yamman Asabar bayan shafe kwanaki 103 a kasar Britaniya ya na ganin likitocinsa.
Mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne ya ci gaba da rike rangamar mulkin tun a wancan lokacin zuwa dawowar shugaban kasar.
Discussion about this post