Buhari ya dage taron Majalisar Zartaswa don ya karbi rahoton binciken harkallar su Babachir

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dage taron mako-mako na Majalisar Zartaswa saboda ya karbi rahoton binciken harkallar Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal da na Shugaban Jami’an Leken Asiri Ayodele Oke.

Kakakin Yada Labaran Shugaban Kasa, Femi Adesina ne ya bayyana haka a safiyar Talata, inda ya ce kwamitin binciken a karkashin shugabancin Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne su ka yi binciken.

Kamata ya yi a ce tun ranar 8 Ga Mayu, 2017 ne ya karbi rahoton, amma sai Buhari ya tafi hutun jinya tun a ranar 7 Ga Mayu.

Ana zargi Babachir da hannu wajen karkatar da kwangilar datse ciyawa har ta naira milyan 250 ga kamfanin sa. Shi kuma Oke ana neman bayanin yadda aka samu tulin kudaden kasashen wajen a wani gida a Legas, wadanda aka ce daga ofishin sa aka karkatar da kudin.

Share.

game da Author