Wasu da ake zargi Boko Haram ne, sun kai mummunan hari a garuruwan Adamawa biy ranar Litinin.
Mazauna yankunan dai sun tsere yayin da Boko Haram su ka kai hari a Nyibango da Muduhu da ke cikin karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa.
Wannan hari dai ya afku ne kwanaki kadan bayan an kai irin wannan mummunan harin a kauyen Mildu da ke makwabtaka da Nyibango, dukkan su a ckin karamar hukuma daya.
Da yake magana kan harin, Shugaban Karamar Hukumar Madagali, Yusuf Muhammad, ya bayyana cewa maharan sai da su ka shafe awa biyu suna hare-hare a garuruwan.
Yace sun kashe dabbbobi, sun kone gidaje masu yawan gaske, sannan kuma su ka yi awon gaba da kayan abinci masu tarin yawa.
Muhammad yace ba zai iya cewa ga yawan wadanda aka kashe ba, domin wadanda su ka tsere daga kauyukan har yau basu dawo ba.
Wani mazaunin yankin mai suna Hamma Adamu,wanda ya gudu, yace maharan sun rika yin harbin kai-mai-uwa-da-wabi, sannan su ka ci gaba da kona gidaje da wuraren ibada
An dai kai wannan hari ne a lokacin da mutanen yankunan ke shirin kwantawa barcin dare.
Dan majalisar tarayya mai wakiltar Madagali/Machika, Adamu Kamale, ya tabbatar da kai wannan hari a yankin na sa. Ya kuma ce hare-haren su na kara tsananta sosai.
An kiyasta akalla mutane dubu 100 daya sun mutu sanadiyyar hare-haren Boko Haram tun daga 2009 zuwa yau.