Yau Talata ne zagayowar ranar haihuwar wadansu fitattun ‘yan fim hudu.
Wadannan fitattaun ‘yan fim din dai sun hada da shahararren dan wasa kuma furodusa, Ibrahim Mandawari, wanda a yanzu shi ne ke rike da sarautar Mai’unguwar Mandawari, cikin Birnin Kano.
Sai kuma fitaccen dan wasa kuma dirakta Ishaq Sidi Ishaq da kuma darakta mai tashe, Hassan Giggs.
Dukkan su an haife su ne a ranar 15 Ga Augusta.
Na cikon hudun shi ne tsohon editan Mujallar Fim, kuma kwararren mai daukar hotunan nan da ke tashe a Arewacin kasar nan, musamman a Kano, Sani Mohammed Maikatanga.