Shugaban Jami’ar Maryam Abacha da ke Kasar Nijar Dr Adamu Gwarzo ya ce ba kamar yadda mutane ke ta yada zance ba cewa wai jami’ar mallaki iyalan tsohon shugaban Kasa Sani Abacha ne, hakan ba daidai bane.
A hira da yayi da manema labarai a lokacin liyafar yaye daliban jami’ar a Nijar, Dr Adamu yace babu ko sisin kwabon Iyalan Abacha wajen kafa jami’ar.
” Na sa sunan Maryam Abacha ne saboda ita uwa ce a gareni. Amma ba ta da wani alaka b ayan haka da wannan Jami’a.” Inji Dr Adamu.
Bayan haka kuma yayi kira ga wadanda suke tambayar inda za su sami fom din shiga jami’ar a Najeriya kamar haka ” Muna da wakilan mu a ko ina a fadin Najeriya sannan muna ba ‘yan Najeriya tallafi domin yin karatu a Jami’ar.”
Dr Adamu ya ce jami’ar Maryam Abacha ce jami’a ta farko da take wata kasa amma ana biyan kudin makarantar da Nairan Najeriya.