An yanke wutar Sakateriyar Karamar Hukuma saboda bashi

0

Hukumar Raba Wutar Lantarki ta Ibadan, IBEDC ta yanke wutar Karamar Hukumar Irepodun jihar Kwara, tun shekara hudu da suka gabata sanadiyyar kasa biyan kudin wuta har na naira miliyan 4.8.

Kamfanin Dillancin Labarai NAN ne ya ruwaito labarin.

Wasiu Sanni, wani Janar Manajan Hukumar IBEDC na Omu-Aran, ya shaida wa NAN cewa karamar hukumar ta ki cika dukkan wasu alkawurra da ta dauka bayan zaman kulla yarjejeniyar yadda za ta rika biyan kudin da kadan-kadan.

“To mu kuwa idan har bashi ya yi matukar yawa, babu wani abu da kamfani zai iya yi, sai dai ya datse wutar kawai.

“Amma ba a son ran mu ba ne a ce mun hana kwastomomin mu wuta, musammamn karamar hukuma.

Shugaban Karamar Hukumar, Jacob Abiodun, ya tabbatar da cewa karamar hukumar ta shafe shekaru hudu babu wutar lantarki, inda ya kara da cewa, hakan na da nasaba da rashin kudi, amma ana kokarin shawo kan lamarin.

Share.

game da Author