Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da tsohon ministan Kwadugo Hussaini Akwanga a gonarsa dake Wamba jihar Nasarawa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kennedy Idrissu ne ya sanar da haka in da ya ce an sace tsohon ministan ne a gonar sa dake titin Wamba, Jihar Nasarawa.
Kennedy ya ce jin haka ke da wuya sai kwamishinan yan sandan jihar Abubakar Sadiq Bello da kansa ya kama hanyar zuwa Akwanga domin neman wadanda suka sace tsohon ministan.