An kulle kasuwar Wuse, Abuja

0

Sanadiyyar arangama da akayi tsakanin matasa ‘yan Kasuwar Wuse da Charly Boy, Jami’an tsaro sun sanar da rufe Kasuwar yau.

Charly Boy ya sha da kyar yau a Kasuwar yayin da ya je cikin kasuwar domin gudanar da zanga-zangar Buhari ya dawo ko ya yi murabus.

Farawar sa ke da wuya sai matasa su ka far masa. Nan da nan su ka fara yi masa ihu su na “ba ma yi, sai Buhari.”

Matasan kuwa suka fara jifarsa da duwatsu, shi kuma ya arce a guje zuwa ofishin ‘yan sanda da ke cikin kasuwar.

Ganau ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa a gaban sa matasa wadanda yawancin su ‘yan dako da masu tura baro ne, su ka biyo Charly Boy da jifa, shi kuma ya na gudu kamar ran sa zai fita.

Bayan kura ta dan lafa, jami’an tsaro sun yi nasarar fitar da Charley Boy daga kasuwar shi da sauran ‘yan rakiyar sa da su ka hada har da masu daukar hoto na bidiyo din da ya je da su.

PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa an samu karin jibgin jama’an tsaro, wadanda su na zuwa su ka bayar da umarnin rufe kasuwar, wadda ita ce mafi girma a Abuja, su ka hana shiga da kuma fita.

Bayan awa daya da rufe kasuwar, ‘yan sanda sun yi amfani da lasifika a daidai karfe 12:20 na rana, inda su ka bayar da umarnin cewa an rufe kasuwar, don haka duk wani da ke cikiya fito ya tafi gida.

A daidai lokacin da ake rubuta wannan labara, cincirindon jama’a sun kafa layukan fita daga cikin kasuwar bisa bin umarnin da aka yi musu cewa kowa ya fice.

Share.

game da Author