An kori ‘yan sanda hudu a kan satar kayan Jonathan

0

Rundanar ‘Yan sandan Babban Birnin Tarayya, Abuja, ta kori wasu ‘yan sanda hudu bayan ta same su da hannu dumu-dumu da laifin dibga sata a wani gidan tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, da ke Gwarimpa, Abuja.

Kwamishinan ‘Yan sandan Abuja, Musa Kimo ne ya amince da korar ta su, a kan laifin yi wa gidan Jonathan karkaf.

Wadanda korar ta shafa sun hada da Sajen Musa Musa, mai lamba 436601; John Nanpak, mai lamba 235422; Ogah Audu, mai lamba 26198 da kuma Gabriel Ugah, mai lamba 425210.

Takardar da kakakin hulda da jama’a na rundunar, Anjuguri Manzah ya sa wa hannu da yammacin Alhamis, ta bayyana cewa ‘yan sandan an damka musu amanar gadin gidan tsohon shugabann kasar, amma sai suke zagayewa su na sace kayan gidan, inda su ka sace komai da ke cikin gidan karkaf.

Ya ce an kore su ne bayan an yi masu wata kwarya-kwayrar shari’a irin wadda ‘yan sanda ke yi ba tare da zuwa kotu ba.

Sanarwar ta kuma ce shi babban dillalin sayar da kayan, wato Sajen Musa, za a gurfanar da shi a kotu, yayin da ake kokarin tabbatar da cewa sai an kamo wani mai suna Sha’aibu, wanda da shi ne Musa ke hada baki.

Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ce ta fara fallasa wannan badakala, inda ta gano kasuwannin da aka rika kai kayan ana sayarwa, ciki har da gadaje, kureru, talbijin da sauran suture mallakar Jonatahan.

Wani binciken mu ya kuma gano yadda ‘yan sandan su ka ribbaci masu sayen kayan su ka yi musu karyar cewa Jonathan ne da kan sa ya raba kayan, bayan an fadi zabe.

‘Yan sanda sun shafe makonni su na kokarin kashec wannan magana kada ta bulla, har sai ranar da PREMIUM TIMES ta fallasa labarin satar, sannan rubdunar ta bayar da sanarwar cewa ta na tsare da wadanda ake zarhin.

A wata sabuwa kuma, akwai sunayen wasu Insufetoci biyu, wadanda aka bayar da sunayen su ga Sufeto Janar na ‘yan sanda, domin ladabtar da su. Saboda girman mukamin su, sai daga can kololuwa ne za a iya hukunta su.

Share.

game da Author