An kama wasu ma’aikatan NAFDAC Uku da laifin sata

0

Hukumar kula da abinci da magunguna na kasa NAFDAC ta sanar da kama wasu ma’aikatanta uku da lafin sace katan-katan din taliya a harabar da hukumar ke kona lalatattun kayayyakin abinci da ta kwato daga hannun mutane ko kamfanoni dake sagamu jihar Ogun.

Jami’in hukumar NAFDAC Kingsley Ejiofor ya sanar da hakan wa manema labarai ranar Laraba.

Ya ce hukumar za ta hukunta ma’aikatan wanda ya hada da Kabiru Amar, Yusuf Ahmed da Mohammed Ibrahim bisa ga laifin da suka aikata.

‘‘Ma’aikatan sun nuna yadda mutum zai iyayin komai domin ya cuci dan ‘uwansa ta hanyar siyar masa da lalatattun abinci’’.

Share.

game da Author