Rundunan ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani magidanci mai suna Ini Udoh da lafin lalata da wasu yan mata kanana uku wanda duk basu wuce shekaru 9 zuwa 12.
Jami’in kula da harka da jama’a na rundunar ‘yan sandan Abimbola Oyeyemi ya fada wa gidan jaridan PREMIUM TIMES cewa sun kama Ini Udoh da ke da shekaru 43 bayan karan da mahaifiyyar ya’yan ta kawo ofishin su dake Sango.
Oyeyemi ya ce mahaifiyar yaran ta dago cewa wani abu makamancin haka na faruwa da daya daga cikin yan matan ne bayan ta ga tabon maniyya a jikin kayan daya daga cikinsu a lokacin da suke wanki a tsakar gidan. Da ta tambaye ta mene wannan abu haka a jikin kayan ta sai yar tace ai makwabcinsu ne ya ke garzayowa da zaran sun fita yana lalata da su.
Oyeyemi ya ce za su ci gaba da gudanar da bincike akan al’amarin sannan sun aika da yaran asibiti domin duba lafiyarsu.
Discussion about this post