An kama motar jami’a dankare da buhunnan ganyen wiwi

0

An kama wata motar bas dankare da buhunnan ganyen wiwi.

Motar dai mallakar Jami’ar Koyon Dabarun Noma ce ta Tarayya da ke Abeokuta, jihar Ogun. Jami’an Kwastan ne su ka kama ta yayin da ta ke safarar fitar da ganyen wiwi a kan iyakar jihar.

Shugaban Rundunar Kwastan na jihar Ogun ne, Sani Madugu ya bayyana haka a yau Talata, yayin da ya ke taro da manema labarai a hedikwatar kwastan ta jihar.

Ya ce kwastan sun jami’an kwastan ne su ka kama direban motar samfurin Coaster, mai tamba: FUNNAB 50 B-100 FG dauke da sunkin wiwi har leda 211.

Madugu, wanda ya samu rakiyar shugaban hukumar yaki da shan muggan kwayoyi na jihar, Bala Fagge, ya ce wanda ake zargin mai suna Abolade Bolaji, an kama shi ne a garin Imeko, yayin da ya ke shigo da wiwi din a cikin kasar nan.

Ya ce ya shigo da tabar ne a cikin buhunnan shinkafa. Tuni dai kwastan su ka damka shi a hannun hukumar hana shan muggan kwayoyi, NDLEA.

A wata sanarwa kuma, jami’ar ta ce ba za ta yi katsalandan a cikin binciken da ake yi wa wanda aka kama da motar da kuma wiwi din ba.

Share.

game da Author