An gurfanar da dan sandan da ya saci kayan gidan Jonathan

0

A yau Talata ne Rundunar ‘Yan sandan Babban Birnin Tarayya, Abuja, su ka gurfanar da jami’in dan sanda Musa Musa, a bisa zargin kwashe kaya a gidan tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Rundunar ta bayyana wa Premium Times haka a ranar Talata din nan.

Musa wanda Sajan ne na ‘yan sanda, ya na daya daga cikin wadanda su ka saci kayan, amma dai a zuwa yanzu shi kadai aka maka kotu.

Wasu daga cikin kayayyakin da aka sata, sun hada talbijin, gadaje da kujeru, kofofi da tagogi, firij, AC, suturu na maza da mata da sauran su.

Bayan an gama jin bayanan mai gabatar da kara da na lauya, mai shari’a Mabel Segun-Bello ta bada belin sa a kan naira milyan bakwai.

An iza keyar sa kurkuku kafin a samu wanda zai amince ya karfi belin nasa.

Share.

game da Author