An cafke limamin cocin da ya damfari mai takaba naira miliyan 500

0

Jami’an ‘yan sandan Jihar Enugu sun bayyana cewa sun samu nasarar cafke wani babban limamin wani coci mai suna Ginika Obi, bayan ya damfani jama’a sama da naira miliyan 500.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ebere Amaraizu ne ya bayyana hakan a wata takardar da ya raba wa manema labarai a ranar Litinin.

Ya ce Bishop Ginika, wanda shi ne limamin cocin City Liberation and Comfort da ke Enugu, ya dade ya na wasan buya da jami’an ‘yan sanda har tsawon wata uku.

Sun kuma bayyana cewa tun bayan da aka cafke shi, ya na nan ya na bada hadin kai yayin da ya ke amsa tambayoyin wani sashen kama masu manyan laifuka na musamman da kwamishinan ‘yan sandan jihar ya kafa.

An cafke shi ne a cikin wani otal da ya shafe watanni ya na boye a ciki.

“Kafin kamun nasa, wanda ake zargin, dan asalin garin Umuaku da ke cikin yankin karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambara, ya taba damfarar wata kungiya mai zaman kan ta mai suna ‘Build Your Generational Organisation’.

Jami’an ‘yan sanda sun ce ya kafa kungiyar ne da zimmar yaudarar mutane cewa idan ka zuba kadan, za ka kwashi mai yawa a can gaba kadan. A haka wadanda tsautsayin asara ya ritsa da su, su ka rika antaya masa kudade, a karshe ya antaya a guje ya bar su a baya.

“Daga baya an daure wasu daga cikin abokan damfarar sa, ciki har da matar sa a kurkukun Enugu.

An yi ta neman Bishop Ginika, inda a karshe aka riktsa shi a wani otal bayan ya damfari jama’a sama da naira milyan 500.

A wani bincike da ake yi masa, ya shaida wa ‘yan sanda cewa naira milyan 186 ne ya san ta damfari jama’a,ba naira milyan 500 ba.

Ana dai ci gaba da binciken sa, kamar yadda Kwamishinan ‘Yan sandan jihar, Danmalam Mohammed ya jaddada.

Share.

game da Author