Amfani 7 da sakuce ko Asuwakin hakora ke yi wa lafiyar mutum

0

Sakucen hakora wata hanyan tsaftace hakora ne idan nama ko abinci ta makale a hokorin.

Likitocin hakora sun ce banda hana warin baki da sakucen hakora ke yi yana kuma kare mutum daga kamuwa da cututtuka.

Ga hanyoyin kamar haka:

1. Likitocin hakora sunce barin abinci ko kuma nama a cikin hakora kamar barin dati ne a cikin baki wanda kan sa cututtuka daga nan ne cutar take samun shiga jikin mutum ta makogoro da jini.

2. Bunkasa garkuwan jikin mutum saboda yin hakan ya toshe kafar da cuta ke shiga jikin mutum.

3. Hana cirewan hakora da sauri wato rage yadda mutum zai iya rasa hakoransa tun kafin mutum ya tsufa.

4. Yana kawar da cutar gabobin jiki.

5. Yana kare mutum daga kamuwa da cutar siga sannan yana rage cutar a jikin wadanda suke dauke da cutar.

6. Yana rage kiba a jikin mutum.

7. Yana kara kuzarin namiji.

Share.

game da Author