Amfani 5 da kwan Salwa ke yi a jikin mutum

1

Salwa wata karamar tsun-tsu ce wanda kwanta ke da matukar mahimmanci a jikin mutum sai dai ba kowa ne ya san hakan ba.

Bincike ya nuna cewa an fi samun tsun-tsayen a kasashen turawa,arewacin Afrika, kudancin kasar Amurka da wasu yankunan kasashen Asia.

Kwan salwa na da kankanta wanda idan ka dafa ta za ka iya cin biyar ko fiye da haka a lokaci daya.

Wasu masanan mahimmancin da kwan a jikin mutum sun ce kwan ya fi aiki a jikin mutum idan an dafa shi ba soya wa ba.

Sun bayyana mahimmancin kwan a jikin mutum kamar haka;

1. Yana kara karfin idanu domin yana dauke da sinadarin Vitamin’A’ wanda ta fi na kwan kaza ko agwagwa yawa.

2. Yana kara kiba musamman ga wadanda suke bukata.

3. Yana taimaka wa jikin mutum wajen fitar da aben da jikin baya bukata kamar su fitsari, bahaya, zufa da sauransu.

4. Yana dauke da sinadarin ‘Protein’ wanda ke kara jini, karfin kashi da girman jikin mutum musamman yara kanana.

5. Yana kuma kara karfi a jiki.

Share.

game da Author